Hukumomi a Jamhuriyar Nijar sun bayyana damuwarsu kan ƙaruwar fasa-ƙwaurin miyagun ƙwayoyi a tsakanin iyakokin ƙasarta da Najeriya da kuma Jamhuriyar Benin.
Hakan na zuwa ne bayan da aka kama ɗaruruwan ɗaurin tabar wiwi da wata ƙwaya nau’in baliyam mai hatsari, da aka yi yunƙurin shigar da su ƙasar a ranar Juma’a daga wata ƙasa mai maƙwabtaka da su.
Shugaban gundumar Gaya a cikin jihar Dosso, da ke Kudu Maso Yammacin Nijar, Ashimu Abarshi, ne ya yi wa manema labarai ƙarin bayani game da kama miyagun ƙwayoyi da ka yi.
Ya ce ƙwayoyin da suka kama sun haɗa da tabar wiwi ɗauri 400 da kuma ɗauri 1,260 na wata ƙwaya mai suna Diezepam, da ɗauri biyar na ganyen wiwi, da aka yiwo fasa-ƙwaurinsu a cikin kwale-kwale ta Kogin Isa.
Jami’in ya ce a baya-bayan nan, sun lura masu fasa-ƙwaurin ƙwayoyi na ƙara ƙaimi wajen safarar miyagun ƙwayoyi ta cikin Jamhuriyar Nijar.
Ashimu Abarshi bai bayyana ƙasar da suke zargin ake shirin shiga da ƙwayoyin ba daga Nijar, amma ya tabbatar da cewa ƙwayoyin sun fito ne daga Jamhuriyar Benin da Nijar da kuma Najeriya.