Ƙungiyar ɗaliban Najeriya ta ƙasa, NANS ta mara wa ƙungiyoyin ƙwadago na NLC da TUC baya kan yunƙurinsu na gwanin gwamnatin tarayya ta ƙara mafi ƙarancin albashi a ƙasar nan.
Wannan na zuawa ne a lokacin da ƙungiyon ƙwadagon suka sha alwashin tsunduma yajin aiki daga gobe Litinin saboda abin da suka kira da “ƙin amincewar gwamnati wajen ƙara kuɗin da ta yi alƙawarin biya na Naira 60.
A sanarwar da ƙungiyar ɗaliban ta ƙasa ta fitar, ta roƙi gwamnatin tarayya da ta gaggauta amincewa da buƙatar ƙungiyoyin ƙwadagon domin ka da ayyukan koyo da koyarwa da ma sauran ayyuka a ƙasar nan su dakata, inda ya ci gaba da cewa za su mara wa ƙungiyoyin baya wajen samun adalci.