Home » ‘Yan Sanda sun Cafke Wani Direban Motar bas a Legas

‘Yan Sanda sun Cafke Wani Direban Motar bas a Legas

Jihar Lagos/Hukumar ‘Yan sanda

by Anas Dansalma
0 comment

Caji ofis din ‘yan sanda da ke layin dogo a Jihar Lagos ya sanar da cafke direban motar bas da ya dauko ma’aikatan gwamnatin jihar, biyo bayan taho mu gama da bas din ta yi da wani jirgin kasa da ke kan tafiyar sa a jiya Alhamis.

Majiyarmu ta ruwaito cewa, fasinjoji shida ne suka mutu a hatsarin wanda aka dora laifin kan sakacin direban.

Direban mai suna Oluwaseun Osinbajo, ya tuko motar ce daga yankin Isolo zuwa Alausa da ke Ikeja inda yaki tsayar da motar a kan hanyar layin dogo wanda hakan ya janyo motar ta yi taho mu gama da jirgin kasan.

Kwamishinan ‘yansanda na jihar Yetunde Longe ne ya tabbatar da kama direban, inda ya ce, bayan sun gudanar da bincike da daukar sauran bayanai za su gurfanar da direban a gaban kotu.

Kwamishin ya ci gaba da cewa, amma kafin su gurfanar da shi a gaban kotun za su fara kai maganar a gaban daraktan gabatar da hukunci ganin cewa, direban ma’aikacin gwamnatin jihar ne.

Ya ce, rundunar na ci gaba yin bincike don gano yawan wadanda suka mutu a hatsarin, inda ya kara da cewa za kuma a binciki gawarwarkin wadanda suka mutu.

Ya kuma tabbabatar da cewa za su mika direban ga likitoci don su duba kwakwalwarsa ganin cewa, an tsayar da shi, amma yaki tsaya wa wanda hakan ne ya haifar da haɗarin da aka samu. 

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai mai cikakkiyar rajista wadda manufarta ita ce ilimantarwa, da wayar da kai da Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.
Muna nan a kan titin Guda Abdullahi gida mai lamba 19 a Farm Centre, jihar Kano.

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi

©MuhasaTVR 2023. Ku nemi izini kafin yin amfani da duk abin da aka wallafa a wannan shafi

Are you sure want to unlock this post?
Unlock left : 0
Are you sure want to cancel subscription?