Allah ya yi wa Tsohon alƙalin alƙalan kotun ɗaukaka ƙara ta shari’ar musulunci ta jihar Kwara rasuwa, mai shari’a Abdulmutallib Ahmad Ambali.
Marigayin ya rasu ne a safiyar yau Alhamis a asibitin koyarwa na jami’ar Ilorin (UITH), Oke-Oyi, bayan ƴar gajeruwar rashin lafiya. Ya rasu yana da shekara 83 a duniya.
Marigayin shine alƙalin alƙalai na biyu bayan mai shari’a Abdulkadir Orire, kuma rajistara na farko a kotun ɗaukaka ƙara ta shari’ar musulunci a jihar Kwara.
Marigayi Abdulmutallib Ahmad Ambali ya kwashe shekara 8 a kujerar alƙalin alƙalan daga shekarar 2001 zuwa 2008.
A wata tattauna ta manema labarai, alƙalin alƙalan musulunci na jihar Kwara, mai shari’a Abdullateef Kamaldeen wanda ya tabbatar da rasuwar, ya bayyana marigayin a matsayin mutum mai tsoron Allah, haziƙin alƙali wanda yayi riƙo da koyarwar addinin musulunci.
Ya bayyana marigayin a matsayin mutumin kirkiri, mai riƙo da addini, mai kyawawan halaye wanda baya raina kowa.