Abdulkarim Chukkol ya zama mai rikon shugaban hukumar EFCC, biyo bayan dakatar da AbdurRashid Bawa da shugaban kasa Bola Ahamad Tinubu yayi.
Sanarwa mai dauke da sa hannun daraktan yada labarai na ofishin sakataren gwamnati Willie Bassey, da aka fitar a jiya, ta umurci Bawa da ya mika wa daraktan ayyuka na hukumar ta EFCC.
A shekarar 2003 Chukkol ya fara aiki da hukummar EFCC, inda ya kai ga zama babban jami’in bincike da kuma daraktan ayyuka,
Jami’in dan sandan ya taba shugabantar ofishin shiyya na EFCC da ke garin Fatakwal, kafin a mayar da shi hedikwatar hukumar da ke Abuja.