Home » Abuja: Wani Rikici Ya Yi Sanadin Mutuwar Wani a Unguwar Gwarimpa

Abuja: Wani Rikici Ya Yi Sanadin Mutuwar Wani a Unguwar Gwarimpa

by Anas Dansalma
0 comment

Yan sandan babban birnin Abuja sun tabbatar da mutuwar mutum ɗaya a wani rikici da ya ɓarke a unguwar Gwarimpa.

Mai magana da yawun ‘yan sandan Abuja SP Josephine Ade ta faɗa wa Majiyarmu cewa rikicin ya ɓarke ne a tsakanin wasu ƙabilu guda biyu mazauna wani yanki dake Gwarimpa village.

Bayanai sun ce tun a ranar Asabar ne tarzomar ta fara bayan da ƙabilar Gbagyi suka yi yunƙurin korar wasu da suke zargin suna dillancin ƙwayoyi ne a yankin.

‘Yan sanda sun ce mutumin da aka kashe matashi ne ɗan shekara 20, kuma ya rasu ne sanadin raunukan da aka ji masa a jiya.

Sun ce rikicin ya sake tashi da safiyar Litinin, bayan Hausawa sun samu labarin rasuwar ɗan’uwan nasu da aka kai asibiti sanadin raunukan da ya ji, ko da yake sun yi ƙoƙari, a cewar Josephine wajen shawo kan al’amuran.

Ta ce ba gaskiya ba ne jita-jitar da ake yaɗawa cewa Fulani da makiyaya ne suka kai hari unguwar Gwarimpa da ke cikin birnin Abuja.

Wasu kafofin yaɗa labarai sun ba da rahoton cewa faɗan ƙabilancin ya yi sanadin mutuwar mutum uku, zargin da mai magana da yawun ‘yan sanda ta ce shi ma babu ƙanshin gaskiya a ciki.

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai mai cikakkiyar rajista wadda manufarta ita ce ilimantarwa, da wayar da kai da Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.
Muna nan a kan titin Guda Abdullahi gida mai lamba 19 a Farm Centre, jihar Kano.

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi

©MuhasaTVR 2023. Ku nemi izini kafin yin amfani da duk abin da aka wallafa a wannan shafi

Are you sure want to unlock this post?
Unlock left : 0
Are you sure want to cancel subscription?