A yayin da aka cigaba da taron Majalisar Dinkin Duniya karo na 78, shugaba Bila Ahmad Tinubu ya gabatar da jawabinsa a zauren Majalisar.
A cikin jawabin nasa, shugaban ya yi kira ga sauran ƙasashen duniya, musamman na yammacin Turai da daina ɗaukar yankin Afirka a matsayin yanki mai ƙunshe da matsaloli.
Inda ya buƙace su da su ɗauki Afirka a matsayin ƙawa kuma abokiyar hurɗa, ba abin tausayawa ba.
Shugaba Tinubu ya bayyana Afirka a matsayin jigo ga cigaban duniya kamar sauran ƙasashen duniya tare da jan hankalin sauran ƙasashe da su yi aiki da yankin na Afirka.
Shugaban dai ya samu rakiyar matarsa, Remi Tinubu da ma sauran muƙarrabai a gwamnatinsa.