• Home  
  • Aiki muka zo yi wa ‘yan Najeriya ba sharholiya ba ~ Shugaba Tinubu
- Labarai

Aiki muka zo yi wa ‘yan Najeriya ba sharholiya ba ~ Shugaba Tinubu

A cewarsa, gwamnatinsa za ta dinga yin shawara da tattaunawa ba tare da yin ƙarfa-ƙarfa ba wajen yanke hukunci, domin samun kyakkyawar mafita.

Aiki muka zo yi wa 'yan Najeriya ba shan mulki ba ~ Shugaba Tinubu

Sabon ƙasa Shugaba Bola Tinubu ya tabbatar wa ‘yan Nijeriya cewa gwamnatinsa jagoranci tazo yi ba mulkan ‘yan Nijeriya ba.

Ya bayar da wannan tabbacin ne a yau a cikin jawabinsa na karɓar mulki bayan rantsar da shi a matsayin shugaban Nijeriya na 16.

A cewarsa, gwamnatinsa za ta dinga yin shawara da tattaunawa ba tare da yin ƙarfa-ƙarfa ba wajen yanke hukunci, domin samun kyakkyawar mafita.

A cewarsa, yana tare da kowa kuma ba zai bi son zuciyarsa ba akan ra’ayoyin al’umma.

Sannan ya ƙara da cewa sun zo ne domin mu kara gyarawa da kuma warkar da wannan al’umma, ba wai tarwatsa al’umma ba.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai