Uwar gidan shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, Hajiya Aisha Buhari, ta ce, daga yanzu babu buƙatar wani shugaban Najeriya ya fita ƙasar waje domin duba lafiyarsu.
Hajiya Aisha Buhari, ta bayyana haka ne bayan da shugaba Buhari, ya ƙaddamar da sabon sashen duba lafiyar shugaban ƙasa da aka gina a asibiti a fadar mulki ta Villa wanda aka kashe wa naira biliyan 21.
Ta ce an samar da asibitin ne tun shekaru 6 baya, bayan da maigidanta ya jima yana zaman jinya a ƙasar waje.
Haka kuma, ta bayar da tabbacin cewa samar da asibitin ya wadatar da shugabannin Najeriya da iyalansu buƙatar fita waje neman magani ba, amma za su iya fita waje ne kawai don taimaka wa abokan aikinsu a ƙasashen waje.