Uwargidan shugaban kasa Haj. Aisha Buhari ta zagaya da uwargidan zababben shugaban kasa Sanata Oluremi Tinubu fadar shugaban kasa don ta ga zubin fadar.
Yayin da Shugaban Najeriya mai baring ado Muhammadu Buhari ya yi kaura zuwa wani sashe na Fadar Shugaban kasa da ake kira Glass House.
Uwargidan shugaban Aisha Buhari ce ta bayyana hakan a wani bidiyo da ta wallafa a shafinta na Instagram, wanda ya nuna yadda ta tarbi uwargidan zababben shugaban kasa Sanata Oluremi Tinubu inda ta zagaya da ita fadar shugaban kasar.
A ranar 29 ga watan Mayu Buhari zai mika mulki ga Ahmed Bola Tinubu wanda ya lashe zaben da aka yi a watan Fabrairu, ko da yake, ‘yan adawa na kalubalantar sakamakon a kotu.