Wata ƙungiya mai zaman kanta ta ƙasa da ƙasa, TAF Africa, ta shirya wani taron wayar da kan nakkasassu a jihar Kogi kan yadda za su iya taka cikakkiyar rawa a zaɓen gwamnan jihar da za a yi ranar 11 ga watan Nuwamba mai zuwa.
Majiyoyi sun bayyana cewa an yi gangamin wayar da kan nakasassun ne a jihar Kogi da nufin taƙaita rashin sha’awar fita zaɓe, da kuma nuna wa duniya cewa daidai ne a dama da nakasassun jihar a zaɓen gwamnan da ke tafe.
Ɗaya daga cikin ƴan ƙungiyar TAF Africa, Mista Olayemi Samuel ya ce gangamin da suka ƙaddamar a birnin Lokoja ya nuna wa nakkasassu cewa damawa da su a zaɓen gwamnan jihar Kogi na da mahimmanci ga cigaban demokraɗiyyar ƙasar nan.
Mista Samuel ya yi ƙarin haske da cewa, yana da matuƙar mahimmanci a dama da nakkasassu a zaɓen gwamnan jihar Kogi da ke tafe; Yace hakan zai taimaka sosai wajen bai wa wani rukuninsu ƴancin yin zaɓe, kuma su ma har a zaɓe su, su wakilci al’umma.
Yace hakan ba zai iya samuwa ba, sai an wayar musu da kai game da ƴancinsu da hakkokinsu, da kuma yadda ake yin zaɓe don su yi wa abin kyakkyawar fahimta kuma shiga gaba gaɗi a dama da su.
Misiz Egwemi Attah, jami’a a Sashen kula da harkokin nakkasassu a Hukumar Zaɓe Ta Ƙasa Mai Zaman Kanta, INEC, reshen jihar Kogi, ta ce Hukumar ta yi duka shirye-shiryen da ake buƙata, kuma an tanadi duka kayan zaɓen da za su taimaka wa nakkasassu suma su yi zaɓe.

Ta yi kira ga duka nakkasassun da ba su da katin zaɓen dindindin, da su hanzarta su yi rajista, tunda akwai sauran lokacin yin rajista, don su samu damar yin zaɓe.
Da yake jawabi a wajen gangamin wayar da kan nakkasassun na jihar Kogi, shugaban hukumar wayar da kan jama’a da sasanta al’umma, Mista Idris Miliki ya ƙalubalanci nakkasassun su san ƴancinsu kuma su yi amfani da shi. Yace da su, sai sun waye game da abubuwan da ke faruwa a yankunansu, sun san me ake ciki, in ba haka ba zai yi matuƙar wahala su iya tashi su nemi hakkokinsu.
Mista Idris Miliki yace abin takaici ne yadda akasarin nakkasassu ba su san dokoki da ƙudirorin da ke ba su dama ba, kamar dokar da aka yi takanas saboda su a shekarar 2018, da kuma sabuwar dokar zaɓen shekarar 2022. Maliki ya ba su shawarar cewa dole su yunƙura su san waɗannan dokoki.
A nasa ɓangare shugaban ƙungiyar Nakkasassu ta Haɗin Gwiwa Ta Ƙasa, reshen jihar Kogi, Mista Solomon Yahaya, kokawa ya yi da yadda al’umma ke ƙyamar nakkasassu, suna kyarar su tare da yin watsi da su, kuma ya yi kira cewa ya kamata a ga canji.
Mista Solomon Yahaya wanda ke fama da makanta ya jinjina wa ƙungiyar TAF Africa, saboda gangamin da ta shirya na wayar musu da kai, sannan ya yi kira a yi wa nakkasassu gaskiya da adalci a cikin tsare-tsaren zaɓen ƙasar. Har wa yau kuma ya jaddada cewa akwai buƙatar bai wa nakkasassu tsaro da kariya daga abokan hamayya da kuma ɗaiɗaikun ɓata-gari a lokutan zaɓe.
