Mataimakin gwamnan jihar Jigawa kuma ɗan takarar gwamnan jihar a jam’iyyar APC mai mulki, Alhaji Umar Namadi ya lashe zaɓen gwamnan jihar da ya gudana a shekaranci
Namadi ya lashe zabe a ƙananan hukumomi 26 daga cikin 27 na jihar.
Ya samu kuri’u 618,449 inda ya samu galaba a kan ‘yan takarar jam’iyyar PDP, Mustapha Sule Lamido da kuma NNPP Aminu Ibrahim wanda ya zo na uku.
Dan takarar PDP ya samu kuri’u 368,726 a yayin da ɗan takarar NNPP ya samu ƙuri’u 37,156.
Babban jami’in da ke kula da zaben, Farfesa Zaiyanu Umar ne ya sanar da sakamakon zaben a ranar Lahadi.
Ya kuma bayyana nasarar da ya yi a matsayin nufi ne na Allah.
Inda ya gode wa Allah kan nasarar da ya samu da kuma al’ummar jihar Jigawa saboda irin jajircewar da suka nuna a zaɓen da aka gudanar na gwamna a jihar.
Zaɓaɓɓen gwamnan ya kuma buƙaci al’umma da su kasance masu yawaita addu’a and ya tabbatar da cewa zai ɗora daga inda magabacinsa, Alhaji Muhammad Badaru Abubakar, ya tsaya ta fuskar samar da ingantacciyar gwamnati.