A cigaba da bikin ƙaddamar da kanfanin na Dangote, shugaban gamayyar kanfanin Dangote, Aliko Dangote, ya gode wa shugaba Buhari bisa ƙarfafa masa guiwa wajen kai wa ga kammala kafa matatar man fetur irinta ta farko a Afirka.
Dangote ya bayyana hakan ne a yayin bikin ƙaddamar da aikin kammala kanfanin Tace Man da aka yi yau a jihar legas.
Inda ya bayyana cewa ya fara wannan yunƙurin kafa wannan kanfani ne a ‘yan shekarun baya, sai dai ya yi ta gamuwa da matsaloli masu yawan gaske.
Sai dai a yanzu ya yi matuƙar farin ciki bayan da mafarkinsa ya zama gaskiya.
Sannan Dangote ya gode wa gwamnatin jihar legas tun daga tsohon gwamnan jihar Bola Tinubu wanda ya jagoranci jihar daga shekarar 1999 zuwa 2007 zuwa ga gwmna mai ci Babajide Sanwo-Olu bisa gudunmuwar da suka ba shi.