Amurka ta ce za ta ƙyale ƙawayenta na Nahiyar Turai su bai wa Ukraine jirgin yaƙin da ta ƙera na F-16.
Mai bai wa shugaban Amurka shawara kan tsaro, Jake Sullivan, ya ce Shugaba Joe Biden ya faɗa wa taron ƙasashen mafiya girman tattalin arziki a duniya da akafi sani da G7 game da matakin yayin taron da suke gudanarwa a Japan yanzu haka.
Sojojin Amurka za su bai wa na Ukraine horo kan yadda za su yi amfani da jiragen .
Ukraine ta daɗe tana neman manyan makamai na zamani daga ƙawayen nata, kuma Shugaba Volodymyr Zelensky ya yabi matakin da cewa mai cike da tarihi.
Ƙasashen da suka mallaki irin waɗannan makamai ko jirage ba za su iya sayarwa ko kuma kai su wata ƙasa ba sai da amincewar Amurka.