Home » An Ɗage Dokar Haramta Wa Ƴan Najeriya Biza

An Ɗage Dokar Haramta Wa Ƴan Najeriya Biza

by Halima Djimrao
0 comment

Haɗaɗɗiyar Daular Ƙasashen Larabawa, UAE,  ta ɗage dokar haramta bada biza ga ƴan Najeriya.

Haramcin wanda ya kai tsawon watanni 10 ya shafi al’amuran ƴan Najeriya da dama masu yawan zuwa Haɗaɗɗiyar Daular Ƙasashen Larabawar don yin harkokinsu na kasuwanci ko yawon shaƙatawa da buɗe ido.

Mai bai wa shugaba Tinubu shawara kan harkokin yaɗa labarai Ajuri Ngelale ya fitar da wata sanarwar cewa UAE ta ɗage haramcin ne bayan ganawar da Tinubu ya yi da shugaban ƙasar Mohamed bin Zayed Al Nahyan Litinin ɗin nan.

An cimma yarjejeniyar ce mai ɗimbin tarihi wadda ta kai ka ɗage haramcin bayar da biza ga ƴan Nijeriya ba tare da ɓata lokaci ba, kamar yadda Ajuri Ngelale ya faɗa a cikin sanarwar.

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai dake da cikakkiyar rejista da ke da manufa ta ilimantarwa, wayar da kai Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.

Ofishinmu yana nan a kan titin Guda Abdullahi dake Farm Centre a jihar Kano. 

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi