Hukumar Tsaro Ta Farin Kaya (DSS) ta kama shugaban karamar hukumar Obi da ke Jihar Nasarawa Hon. Joshua da tarin takardun zabe na bogi wadanda aka riga aka dangwale su.
Lamarin ya faru ne a yau ɗin nan a yayin da ake gudanar da zaɓen gwamnoni da na ‘yan majalisun dokoki jihohi a faɗin ƙasar nan.
Jami’an tsaron sun kama Shugaban karamar Hukumar ne a unguwar Tudun Kwauri dake Lafiya ta jihar Nasarawa a kan hanyarsa ta zuwa inda yake shirin kai takardun.
A halin yanzu dai Hon. yana hannu jami’an tsaro.
Duk da wannan al’amari, majiyarmu ta tabbatar mana da cewa a nan ana gudanar da zaɓe a jihar ta Nassarawa.