Majalisar dinkin duniya ta ce an sace abincin agaji da ke cikin motoci kusan 100 da za a kai wa Falasɗinawa ranar 16 ga watan Nuwamba a wani mataki da ake gani yana cikin sata mafi muni a watanni 13 da aka kwashe ana yaƙi a yankin.
Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya bayyana cewa hukumomi biyu na MDD sun bayyana masa cewa yunwa na ƙara ƙamari a Gaza a ranar Asabar 16 ga Nuwamba.
An ce kasar Isra’ila ce ta umarci tawagar da ke ɗauke da kayan abincin da da hukumar UNRWA suka aiko da Shirin Samar da Abinci na MDD su fice daga yankin ba tare da ɓata lokaci ba.
Haka zalika kasar Isra’ila ta ta tilasta musu bi ta hanyar da ba a saba bi ba, wato hanyar Karem Abu Salem, a cewar Louise Wateridge, wata babbar jami’a ta UNRWA.
Jami’a Louise Wateridge ta ƙara da cewa an sace kayan abinci daga cikin motoci casa’in da takwas cikin motoci 109 da ke tawagar kuma an jikkata wasu daga cikin direbobinsu.
“Wannan lamari ya nuna girman ƙalubalen da muke fuskanta wajen kai agaji a kudanci da tsakiyar Gaza,”