Home » An sake gurfanar da gwamnan babban bankin Najeriya, Emefiele da wasu mutane

An sake gurfanar da gwamnan babban bankin Najeriya, Emefiele da wasu mutane

by Anas Dansalma
0 comment
An sake gurfanar da gwamnan babban bankin Najeriya, Emefiele da wasu mutane

Gwamnatin tarayya ta sake gurfanar da Gwamnan Babban Bankin ƙasar nan, Godwin Emefiele da wasu ƙarin mutanan da aka dakatar da su a gaban babbar kotun tarayya da ke Abuja a ranar Alhamis mai zuwa bisa zargin almundahanar Naira biliyan 6.9.

Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da ofishin sakataren Gwamnatin Tarayya ke ƙarar Emefiele bisa badaƙalar kuɗaɗe har naira biliyan 6.9.

A ranar Alhamis, 17 ga watan Agusta ne za a saurari ƙarar da aka shigar da Emefiele a wata babbar kotu da ke zamanta a yankin Maitama da ke Abuja.

Emefiele tare da wata ma’aikaciyar CBN Sa’adatu Yaro da kamfaninta mai suna April1616 Investment Limited, za su gurfana gaban kotu kan tuhume-tuhume guda 20 da ke da alaƙa da badaƙalar kuɗaɗe.

Tsohon gwamnan bankin Emefele wanda ya kasan ce a tsare tun lokacin da aka dakatar da shi daga aiki a ranar 9 ga watan Yunin da ya gabata, ana zarge shi da bayar da cin hanci da rashawa ga Sa’adatu Yaro.

Kuma laifin ya saɓa wa sashe 19 na dokokin cin hanci da rashawa da sauran laifukan da suka shafi doka ta 2000.

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai dake da cikakkiyar rejista da ke da manufa ta ilimantarwa, wayar da kai Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.

Ofishinmu yana nan a kan titin Guda Abdullahi dake Farm Centre a jihar Kano. 

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi