An sako ɗaliban sakandiren Yawuri huɗu cikin mata 11 da suka rage a hannu ƙasurgumin ɗan fashin daji, Dogo Giɗe.
Shugaban ƙungiyar iyayen ɗaliban da suka rage a hannun ‘yan fashin daji, Salim Ka’oje ne ya tabbatar da haka, inda ya ce ‘yan matan huɗu sun kuɓuta ne sanadin wani ƙoƙari da mahaifan ɗaliban da kuma masu tallafa musu suka yi.
Cikin ‘yan matan da suka kuɓuta in ji Salim Ka’oje, akwai Fa’iza Ahmed da Hafsat Idris da Bilham Musa da kuma Rahama Abdullahi.
Ya ce sun yi nasarar karɓo ‘ya’yan nasu ne, kuma yanzu haka sun isa Birnin Kebbi a ƙoƙarin da suke yi na kai su asibiti domin bincika lafiyarsu.
An sako ɗaliban ne a jiya da misalin ƙarfe 4:30
Ɗaliban huɗu sun shaƙi iskar ‘yanci ne bayan sun kwashe kimanin shekara biyu a daji ta hanyar wata gidauniya da iyayen suka kafa.
“Sai da muka kwashe tsawon kwana shida a cikin daji, kafin mu iya karɓar su,” in ji Ka’oje.
Idan za a iya tunawa dai a watan Yunin 2021 ne, ƴan fashin a kan babura suka kutsa Kwalejin Gwamnatin Tarayya ta Yawuri suna harbi da bindiga, kafin su kwashe ɗalibai kimanin 100 bayan sun kashe malami ɗaya.
An sako mafi yawan ɗaliban ne rukuni-rukuni bayan mahaifansu sun biya kuɗin fansa, amma ‘yan fashin suka ci gaba da riƙe ɗalibai mata 11, waɗanda har rahotanni suka ce har an aurar da su.