Home » An Buƙaci ‘Yan Kasuwa da Kafa ‘Yan Sa Kai Na Kashe Gobara a Kasuwanni

An Buƙaci ‘Yan Kasuwa da Kafa ‘Yan Sa Kai Na Kashe Gobara a Kasuwanni

by Anas Dansalma
0 comment

Shugaban Hukumar Kashe Gobara ta ƙasa, Jaji Olola Abdulganiyu, ya kai ziyarar gani da ido domin jajantawa kan gobarar da ta cinye manyan kasuwanni biyu a Maiduguri, inda ya shawarci ‘yan kasuwan da su kafa kungiyar ‘yan kwana-kwana ta sa kai don dakile matsalar.

Ya kuma alakanta yawaitar asarar dukiyoyi da rashin hanyoyin da za su bai wa jami’an agajin gaggawa damar shiga kasuwar domin kashe gobarar.

A cikin wata guda an samu tashin gobara daban-daban guda uku a manyan kasuwanni da kuma shaguna hada da sansanonin ‘yan gudun hijira guda biyu wanda suka auku a jihar Borno. Sai dai wadda ta fi girma itace wacce ta auku a kasuwar Litinin da aka fi sani da Monday Market inda aka yi asarar sama da shaguna dubu 12 da wutar ta cinye kurmus.

Abdulganiyu ya ce idan da masu aikin sa kai sun samu horo yadda ya kamata tare da samar musu da kayan aikin kashe gobara, za su iya dakile tsanani da gobarar ta yi tun kafin isowar jami’an kashe gobara.

Shugaban yace hanya daya tilo da za a iya hana gobarat ita ce tabbatar da cewa an samar da mafi saukin na’urori. Tukunyar kashe gobara (Fire Extinguisher) a kowane dayan wadannan shagunan na iya taimakawa sosai don rage aukuwar gobara.

Ya kuma ba da tabbacin cewa nan ba da dadewa ba jami’ansa za su fara horas da ‘yan kasuwar aikin sa kai kan yadda ake amfani da barguna da na’urorin kashe gobara.

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai dake da cikakkiyar rejista da ke da manufa ta ilimantarwa, wayar da kai Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.

Ofishinmu yana nan a kan titin Guda Abdullahi dake Farm Centre a jihar Kano. 

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi