Malami a sashen koyar da ilimin Akanta na Jami’ar Bayero, Dr. zaharaddeen Salisu Maigoshi shi ne ya bayyana Hakan a Taron da Hukumar Tattara kudaden shiga ta kasa tare da hadin gwuiwar Apropolitant media limited suka shirya a Cibiyar ‘Yan Jaridu ta jihar Kano.
Dr. Zaharaddeen Salisu Maigoshi ya bayyana Yan jarida a matsayin Wanda suke taka rawa wajen fadakarwa tare da ilimantarwa ta bangaren biyan haraji.
Yakara da cewa, Yan jarida su ne suke wayar da kan jama’a domin su san wane haraji ne daga gwamnati, wanne ne wanda ba na gwamnati ba.
Hajiya Aisha Umar Hallliru shugabar Afropolitan media limited ta bayyana cewa Taron anshirya Taron ne domin ilimantar da mahalarta Taron akan irin ƙalubalen da hukumomin da ke da Alaƙa da tattara kuɗaɗen shiga suke fuskanta, tare da bayyana irin matakan da aka dauka wajen magance wannan kalubalen, karkashin jagorancin shugaban hukumar FIRS Mr. Muhammad Nami.
Taron yasamu halartar Yan jarida daga kafafen yada labarai daban daban, Masana harkar tattara haraji, da Kuma Malaman jami’a.