Home » Ana Cigaba da Samun Ƙarin Hukuncin Kisa a Ƙasar Iran

Ana Cigaba da Samun Ƙarin Hukuncin Kisa a Ƙasar Iran

by Anas Dansalma
0 comment

Hukumar kare hakkin bil adama ta Majalisar Dinkin Duniya ta yi Alla-wadai da karuwar hukuncin kisa a ƙasar Iran, ciki har da wadanda ke da hannu a zanga-zangar kasar.

Hukumar ta amince da wani Ƙuduri da ke nuna matukar damuwa kan yadda ake samun karuwar mutanen da ake kashewa ta wannan hanya, ciki har da mutanen da aka yanke wa hukuncin kisa saboda zargin su da hannu a zanga-zangar baya-bayan nan.

Kudirin wanda ya kara wa’adin mai ba da rahoto na musamman na Majalisar Dinkin Duniya kan harkokin kare hakkin bil adama a Iran da tsawon shekara guda, ya samu kuri’un amincewa 23 daga cikin wakilan hukumar 47.

Wasu wakilai 6 sun kaurace wa kada kuri’ar, a yayin da ƘASAR China da Cuba da Pakistan da Vietnam suka kasance cikin kasashe 8 da suka yi adawa da wannan mataki.

Kudurin ya yi nuni da kakkausar suka daga kasashen duniya kan murkushe masu zanga-zangar da kasar ta Iran ta yi a watan Satumban bara.

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai dake da cikakkiyar rejista da ke da manufa ta ilimantarwa, wayar da kai Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.

Ofishinmu yana nan a kan titin Guda Abdullahi dake Farm Centre a jihar Kano. 

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi