Hukumar Gudanarwar Majalisar Dokoki ta Kasa, ta fara shirin biyan Sanatoci da ’yan Majalisar Wakilai masu barin gado kudaden sallama da suka kai Naira biliyan 30.
Akawun majalisar, Yahaya Danzariya, ne ya bayyana hakan yayin zaman majalisar.
Majalisar Dokokin Najeriya ta tara dai wacce aka rantsar ranar 11 ga watan Yunin 2019, ana sa ran kawo karshenta ranar 13 ga watan Yuni, ranar da za a rantsar da sababbi.
Kakakin Majalisar, Femi Gbajabiamila ne ya karanta takardar ga mambobin majalisar yayin zamansu na su.
An dai ware sama da Naira biliyan 30 ga majalisar ta tara mai barin gado da kuma na maraba ga sababbin ’yan majalisa da hadimansu a kasafin kudi na 2023.
A karkashin kasafin dai, majalisun sun ware Naira 194,839,144,401 a bana,
A wani labarin kuma, an ware sama da Naira biliyan daya ga shugabannin hukumomi da ma’aikatun gwamnati, yayin da za a kashe wa tsofaffin Shugabannin Kasa da Mataimakansu Naira biliyan 2.3.