Jam’iyyar APC a Jihar Kano ta shigar da kara a gaban kotun sauraren kararrakin zaben gwamnan Kano da ke zamanta a Miller road, tana kalubalantar nasarar zababben gwamnan Kano, Abba Kabiru Yusuf na jam’iyyar NNPP.
Majiyarmu ta ruwaito cewa an shigar da karar ne a gaban kotun, a ranar 9 ga watan Afrilun da muke ciki.
Jam’iyyar APC ta sanar da kotun cewa, sunan zababben gwamnan jihar, Abba Kabiru Yusuf ba ya cikin jerin rajistar NNPP da ke hannun hukumar ta INEC.
APC ta bayyana a cikin karar cewa kafin zaben gwamna da aka gudanar a ranar 18 ga Maris, dan takarar jam’iyyar NNPP ya gaza cika sharuddan zama mamban jam’iyyar, don haka ake zargin bai cancanci tsayawa takara a zaben gwamna a karkashin jam’iyyar NNPP ba.
Bugu da kari masu shigar da kara sun roki kotun da ta rusa wa’adin zaben Abba.
APC ta bukaci kotun da ta amince da adadin kuri’un da aka kada ba bisa ka’ida ba, don haka a yi la’akari da yadda aka cire adadin kuri’un da aka soke ba bisa ka’ida ba tare da ayyana zaben a matsayin ‘Inconclusive’.
Masu gabatar da kara, sun bukaci NNPP da dan takararta na gwamna da INEC cikin wa’adin kwanaki 21 da su amsa batutuwan da masu shigar da kara suka kai.
A wani lamari makamancin haka, kotun ta bai wa jam’iyyar APC takardar bukatar duba kayan zaben gwamna, a wani bangare na ci gaba da shari’arsu da NNPP a gaban kotu.
Mai ba da shawara kan harkokin shari’a na jam’iyyar APC na Jihar Kano, Abdul Adamu Fagge, ya tabbatar da cewa tawagar jam’iyyar APC ta fara duba kayayyakin zaben da aka yi amfani da su a kananan hukumomi 44 da ke fadin jihar.
A cewarsa aikin duba kayayyakin yana gudana cikin kwanciyar hankali tare da goyon bayan dukkan bangarorin da abin ya shafa.
Ya kuma bayyana kwarin gwiwarsa na cewa babu wata tangarda da ake sa ran za ta kawo cikas ga aikin, inda ya ce zuwa yanzu an ba su damar yin amfani da dukkan kayan, inda ya ce jam’iyyar za ta bibiyi lamarin.