Home » Asari Dakubo Ya Shawarci Shugaba Tinubu Kan Cigaba da Tsare Nnamdi Kanu

Asari Dakubo Ya Shawarci Shugaba Tinubu Kan Cigaba da Tsare Nnamdi Kanu

by Anas Dansalma
0 comment
Asari Dakubo Ya Shawarci Shugaba Tinubu Kan Cigaba da Tsare Nnamdi Kanu

Jagoran tsagerun Neja Delta, Asari Dokubo ya shawarci Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu kan kada ya kuskura ya saki jagoran kungiyar ’yan aware ta Biyafara (IPOB), Nnamdi Kanu.

A cewar Dokubo, bai wa Nnamdi Kanu damar shakar iskar ’yanci zai kasance tamkar yi wa ta’addanci sakayya da tukwici na alheri.

Dokubo ya yi wannan furuci ne a jiya Juma’ar yayin ganawa da manema labarai bayan ganawarsa da Shugaba Tinubu a Fadar Gwamnatin Najeriya da ke Abuja. Ya cewa, dole ne Nnamdi Kanu ya girbi abin da ya shuka ta fuskar shari’a.

“Sakin Nnamdi Kanu zai zama rashin adalci saboda ya taka rawa wajen rura wutar tashin hankalin da aka gani a lokacin zanga-zangar EndSARS.

A halin yanzu dai Nnamdu Kanu na ci gaba da zama a hannun Hukumar Tsaro ta Farin Kaya DSS, inda ake tuhumarsa da laifin ta’addanci tun bayan sake kama shi da aka yi a shekarar 2021.

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai mai cikakkiyar rajista wadda manufarta ita ce ilimantarwa, da wayar da kai da Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.
Muna nan a kan titin Guda Abdullahi gida mai lamba 19 a Farm Centre, jihar Kano.

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi

©MuhasaTVR 2023. Ku nemi izini kafin yin amfani da duk abin da aka wallafa a wannan shafi

Are you sure want to unlock this post?
Unlock left : 0
Are you sure want to cancel subscription?