Kotu ta umarci Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta bar wasu masu katin zabe na wucin gadi su kada kuri’a a zaben gwamnoni da majalisun dokokin jiha da ke tafe ranar 18 ga watan Maris, 2023.
Mai Shari’a Obiora Egwuatu na Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ya ba da umarnin ne bayan wasu ’yan Najeriya biyu sun shigar da karar neman INEC ta bari masu katin zabe na wucin-gadi su yi zaben da ke tafe.
Mai shari’ar Ya ce Kotu na umartar INEC ta bar masu karar su yi amfani da katin zaben wucin-gadi da ta ba su, tunda dai ta yi musu rajista kuma bayanansu na cikin rajistar zabe.
Mai shari’ah Obiora yace Masu kara na da ’yancin amfani da katin zabensu na wucin-gadi a zabe mai zuwa tunda sun riga sun abin da ya rataya a kansu na rajistar zabe kuma bayanansu sun fito rumbun adana bayanai da sauran takardun zabe da INEC ta wallafa.
ya bayyana cewa babu inda kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999 ko Dokar Zabe suka ce masu katin zabe na dindindin kadai ne za su kada kuri’a.
Ya ce hatta sashe na 47 na dokar zabe, katin zabe kawai ya yi magana, bai ce sai na dindindin ba.