Da alama yarjejeniyar tsagaita wuta da aka ayyana tsakanin ɓangarorin mayaƙa biyu da ke gumurzu da juna a Sudan, domin bikin Idin babbar sallah, ta ruguje.
Wata mai aikin agaji, Duaa Tariq ta shaida wa manema labarai cewa an rinƙa jin rugugin manyan bidigogi a wasu sassa na Khartoum, babban birnin ƙasar tun da sanyin safiyar yau.
A ranar Talata ne, shugaban gwamnatin mulkin sojin Sudan, Abdel Fattah al-Burhan ya yi kira ga matasa da su shiga yaƙin da ake yi da mayaƙan RSF.
Sai dai Tariq ta shaida wa manema labarai cewar dakarun RSF ɗin ne suka fi yawa a Khartoum, inda suka mamaye gidaje da kasuwanni da kuma titunan birnin.
Wasu yarjeniyoyin da aka cimma a baya duk sun gamu da naƙasu wanda hakan ya haifar da cigaba da gwabza faɗa da ake yi.