Jirgin farko maniyyata aikin aiki hajji daga ƙasar Bangladesh hudu da kowanne jirgi ke ɗauke da adadin mutane 419 suka iso filin sauka da tashin jiragen sama na Sarki Abudul’aziz da ke Jidda a jiya Lahadi.
Wannan shi ne Hajji na biyu marar shinge na biyu tun bayan annobar kwarano da ta tilasta taƙaita adadin mutane masu zuwa aikin Hajji a ƙasar ta Saudiyya.
Jirgin Maniyyatan na farko dai ya samu tarba da kyautuka daga jami’an hukumar shige da fice ta ƙasar da ma’aikatan Kula da Aikin Hajji da kuma Hukumar Harkokin Ƙasashen Ketare ta Saudiyya.
Tuni dai maniyyatan suka samu shiga manyan motocin bas-bas da za su kai su masaukansu tare da wayar musu da kai za a ayi game da yadda zaman nasu zai kasance a ƙasar cikin harshensu na uwa.
A kwanakin baya dai ƙasar Saudiyya da hadin guiwar hukumomin ƙasar daban-daban suka samar da wani shiri na taimaka wa wasu Ƙasashe bakwai wajen samun sauƙin zuwa aikin Hajji ƙasar da suka haɗa da: ƙasashen Pakistan, Malaysia da Indonesia da Morroco da Bangladesh da Turkiyya da kuma Kwadebuwa daga yankin Afirka.
Ana dai sa ran jiragen maniyyata za su cigaba da suka a Jidda da Madinah har zuwa 4 ga watan Yuni da aka ɗibar wa maniyyata aikin Hajjin.