Home » Barkewar cutar mashako a birnin tarayya Abuja ya sanya mahukunta daukar mataki

Barkewar cutar mashako a birnin tarayya Abuja ya sanya mahukunta daukar mataki

by Anas Dansalma
0 comment
Barkewar cutar mashako a birnin tarayya Abuja ya sanya mahukunta daukar mataki

Cibiyar yaki da cutuka masu yaduwa ta Najeriya ta ce an samu barkewar cutar mashako (Dphtheria) a babban birnin kasar Abuja, bayan da wani yaro mai shekara hudu ya rasu.

Cutar mai saurin yaduwa tana shafar hanci da makogaro ne ta hana numfashi daga nan kuma takan kai ga illata zuciya da kuma sanya kumburi a jikin mutum, inda yawanci take kama yara masu shekara tsakanin biyu zuwa 14.

Rahotanni sun ce yaron da cutar ta kashe ba a yi masa rigakafi ba.

A sanarwar da hukuma ta bayar  ta ce daman an samu bullar cutar a sassan kasar da dama tun a shekarar da ta gabata.

Zuwa yanzu an samu mutuwar mutum akalla 80 daga cikin mutum kusan 800 da aka tabbatar sun kamu da cutar a kusan jihohi takwas na kasar.

Jihohin da aka samu bullar cutar sun hada da Lagos wadda ta fi yawan jama’a da Kano wadda take bi mata da kuma Abuja babban birnin kasar, zuwa karshen watan Yuni na wannan shekara.

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai mai cikakkiyar rajista wadda manufarta ita ce ilimantarwa, da wayar da kai da Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.
Muna nan a kan titin Guda Abdullahi gida mai lamba 19 a Farm Centre, jihar Kano.

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi

©MuhasaTVR 2023. Ku nemi izini kafin yin amfani da duk abin da aka wallafa a wannan shafi

Are you sure want to unlock this post?
Unlock left : 0
Are you sure want to cancel subscription?