Home » Barno: Kungiyar ISWAP ta haramta wa manoma da masunta gudanar da ayyukansu

Barno: Kungiyar ISWAP ta haramta wa manoma da masunta gudanar da ayyukansu

by Anas Dansalma
0 comment
Barno: Kungiyar ISWAP ta haramta wa manoma da masunta gudanar da ayyukansu

DAGA: HAUWA ABUBAKAR SADIK

Kungiyar ‘yan ta’adda ta ISWAP ta haramtawa manoma da masunta da kuma makiyaya a yankunan karamar hukumar Marte a jihar Borno,

An rawaito cewa kungiyar ISWAP ta sha alwashin kawar da duk wanda aka samu a yankunan Katikime, Bulungahe, Kutukungunla, Chikun Gudu, Tumbumma, Guma Kura, Guma Gana da kuma New Marte, bayan sun zarge su da yi wa sojojin Nijeriya leken asiri da taimaka musu da bayanai.

Hakan na zuwa bayan da kungiyar ta’addancin ta yi mummunar asara sakamakon hare-haren da sojojin Nijeriya suka kai a wasu maboyarsu da aka gano a Marte.

Hare-haren ya yi tafiyar ruwa da manyan kwamandojin ISWAP, da dama da lalata kayan aikinsu.

Wasu daga cikin hare-haren da aka kai ta sama sun hada da Grazah da Wa-Jahode, da ke gefen tsaunin Mandara wanda majiyoyin soji suka ce ya an kashe ‘yan ta’adda sama da 100.

Wata majiya ta ce a gabar kogin Jibularam da Sabon Tumbum, harin da SOJIN SAMA ta kai ta sama ya kai ga korar kwamandojin ISWAP guda biyu, Amir Malam Bello da Amir Malam Musa Modu da mayakansu da dama.

Majiyar ta ce an kai wasu hare-hare ta sama a Kwalaram, Bukar Mairam, Abbaganaram da Yarwa Kura, lamarin da ya kai ga halaka mayakan da dama tare da tilastawa wasu tserewa da raunuka a jikinsu.

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai mai cikakkiyar rajista wadda manufarta ita ce ilimantarwa, da wayar da kai da Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.
Muna nan a kan titin Guda Abdullahi gida mai lamba 19 a Farm Centre, jihar Kano.

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi

©MuhasaTVR 2023. Ku nemi izini kafin yin amfani da duk abin da aka wallafa a wannan shafi

Are you sure want to unlock this post?
Unlock left : 0
Are you sure want to cancel subscription?