Babbar Kotun Shari’ar Musulunci mai lamba 1 da ke Jihar Bauchi ta tura Dakta Idris Abdul’aziz Dutsen Tanshi gyara hali har zuwa nan da wata guda, bisa abin da ta kira ‘raini ga kotu’.
Alkalin kotun, Malam Hussaini Turaki, shi ne ya aike da babban malamin zuwa gidan gyara halin a zaman kotun da ya gudana jiya Litinin.
A kwafin umurnin aikewa da Malamin gidan yarin da rahotonni suka bayyana da ke nuni da cewa bisa ga ‘raini ga kotu’ wato ‘Contempt of court’ ne Alkalin ya aike da malamin gidan yari, inda za a dawo da shi gaban kotun a ranar 19 ga watan gobe.
Umurnin da Alkalin ya bai wa babban jami’in kula da gidan yarin na cewa, “An baka izinin ka karbe shi ka tsare shi a gadirum sai an aiko maka da wata oda.”
Umarnin na kotun ya ce idan har ba wani umarnin na daban kuma aka aiko ba, malamin zai cigaba da zama a gidan har zuwa ranar 19 ga watan gobe.