Home » Shugaba Buhari Na Ƙaddamar da Sabbin Launukan Rundunar Sojin Najeriya

Shugaba Buhari Na Ƙaddamar da Sabbin Launukan Rundunar Sojin Najeriya

by Anas Dansalma
0 comment

A yau ne 27 ga watan Afrilu, 2023, Shugaba Muhammadu Buhari yake karɓar faretin addamar da sabbin launuka na rundunonin sojan Najeriya. .

Ana gudanar da bikin kaddamarwar ne a dandalin Eagle Square da ke Abuja babban birnin ƙasar, inda shugaban ya samu rakiyar shugaban ma’aikata na fadarsa, Farfesa Ibrahim Gambari.

An ga shugaba Buhari sanye da kakin soja, inda yake zagayawa don duba sojoji da ke yin faretin.

Babban Hafsan Tsaro, Janar Lucky Irabor da Shugaban Rundunar Sojin Najeriya Laftanar-Janar Faruk Yahaya da Sufeton Ƴan Sanda Usman Alkali Baba na cikin mutanen da suka halarci bikin kaddamarwan.

Sauran waɗanda suka halarci bikin sun haɗa da: Shugaban Rundunar Sojin Sama, Air Marshal Oladayo Amao da Shugaban Rundunar Sojin Ruwa, Rear Admiral Awwal Zubairu Gambo da kuma Shugagan Majalisar Dattawa Ahmad Lawan.

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai dake da cikakkiyar rejista da ke da manufa ta ilimantarwa, wayar da kai Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.

Ofishinmu yana nan a kan titin Guda Abdullahi dake Farm Centre a jihar Kano. 

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi