Zababben shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, ya ce abin da ya fi mayar da hankali a kai shi ne kafa gwamnati mai cike da gogaggun jami’ai ba samar da gwamnatin haɗaka ba wajen magance kalubalen da kasarnan ke fuskanta.
Tinubu ya bayyana haka ne a wata wasika da ya sanya wa hannu da kansa a jiya Alhamis a Abuja.
Tinubu ya ce matsayisa na shugaba mai jiran gado, ya amince da aikin da ke gabansa.
Ya kara da cewa an yi maganar kafa gwamnatin hadin kan kasa, amma shi burinsa ya fi ga haka.
Yace yana neman gwamnati mai cike das ƙwararru ne a mataki na ƙasa.
Hukumar INEC ta ayyana Tinubu a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa da aka yi ranar 25 ga watan Fabrairu.
Kuma tuni tsohon gwamnan jihar Legas ya karbi takardar shaidar cin zabe daga hukumar.
Ana sa ran za a rantsar da Tinubu a matsayin shugaban kasar nan nan da makwanni kadan, wanda zai maye gurbin Shugaba Muhammadu Buhari.