Home » CBN: Majalisar Dattawa ta shiga karatu na II kan ƙudurin shiga siyasar ma’aikata

CBN: Majalisar Dattawa ta shiga karatu na II kan ƙudurin shiga siyasar ma’aikata

by Anas Dansalma
0 comment
CBN: Majalisar Dattawa ta shiga karatu na II kan ƙudurin shiga siyasar ma'aikata

A jiya Majalisar Dattawa ta kammala karatu na biyu na ƙuduri wanda ya shafi babban bankin ƙasar nan, inda aka buƙaci a yi doka da za ta hana duk wani gwaman bankin da ke bakin aiki shiga harkokin siyasa.

Sanata mai wakiltar Yammacin jihar Kogi, sanata Steve Karimi na jam’iyyar APC, ne ya gabatar da ƙudurin, sai kuma makamancin wannan ƙuduri da sanata mai wakiltar jihar Abia ta tsakiya na jam’iyyar LP, shi ma ya gabatar.

A baya-bayan nan an ga yadda tsohon gwamnan babban bankin, Godwin Emefiele, ya shiga siyasa da ta kai ga neman takarar shugabancin ƙasa a jam’iyyar APC a lokacin da yake kan aiki wanda hakan ya jawo cece-ku-ce.

Sanata Karimi ya bayyana cewa, manufar wannan ƙuduri shi ne tabbatar da an tafi da harkokin babban banki yadda ya kamata tare da haramta amfani da kuɗaɗen ƙetare a yayin kasuwanci na cikin gida.
Sannan ya buƙaci a sake duba sashe na 9(2) na kundin CBN wanda ya buƙaci a haramta wa gwamnan babban banki da mataimakinsa shiga harkokin siyasa da neman kowacce irin takara a lokacin da suke riƙe da ofisoshin gwamnati.

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai dake da cikakkiyar rejista da ke da manufa ta ilimantarwa, wayar da kai Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.

Ofishinmu yana nan a kan titin Guda Abdullahi dake Farm Centre a jihar Kano. 

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi