Babban Bankin Najeriya CBN ya ɗage haramcin bayar da canjin dala domin shigo da shinkafa da wasu kayyaki 42 cikin ƙasar nan a wani yunƙuri na tallafa wa kasuwar musayar kuɗi na ‘lokaci zuwa lokaci’.
A shekarar 2015 ne CBN ya taƙaita bayar da dala domin shigowa da wasu abubuwa ƙasar, yana mai cewa bai kamata a bayar da dala domin shigowa da su ba, kasancewar ana iya samar da su a cikin ƙasar.
To sai dai cikin wata sanarwar da CBN din ya fitar ranar Alhamis, mai ɗauke da sa hannun babban daraktan sadarwar babban bankin, Isa Abdulmumin, ya ce kayyakin da aka ɗage wa haramcin sun haɗa da shinkafa da siminti da man ja da nama da
Sanarwar ta ci gaba da cewa a yanzu masu shigo da abubuwa 43 za su iya samun chanjin dala daga babban bankin na CBN.