Babban bankin ƙasar nan ya umarci sauran bankunan kasuwanci na ƙasar nan da su buɗe bankuna a ranakun Asabar ɗin da muke ciki da Lahadi.
Wannan umarni ya fito ne daga bakin daraktan riƙon ƙwarya na hukumar Dr. Isa Abdulmumin wanda ya bayyana cewa tuni suka umarci bankunan kasuwanci da su zuba wadataccen kuɗi a na’urorin ba da kuɗi na ATM tare da buɗe bankunan a ranakun ƙarshen makwan nan.
Wannan na zuwa ne a matsayin wani mataki da babban bankin na ƙasa ya ɗauka domin tabbatar da wadatuwar takardun kuɗi a hannun mutane.
Sannan ya buƙaci al’ummar ƙasar nan da su ƙara haƙuri tare da tabbatar da cewa nan ba da daɗewa ba za kawar da wannan matsala da ke damun al’ummar.