Wata ƙungiya mai zaman kanta mai suna War Against Injustice ta buƙaci hukumar Yaƙi da Masu Yi Tattalin Arziƙin Ƙasa Zagon Ƙasa da ta cafke tsohon gwamnan jihar Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje bisa zargin lafin cin hanci da rashawa.
Kungiyar ta bayyana wa hukumar EFCC cewa a cikin shekarar 2018 ne wani faifan bidiyo wanda editan kanfanin jaridar Daily Nigerian, Jaafar Jaafar ya wallafa da ke nuna yadda tsohon gwamnan jihar Kano Ganduje ke karɓar cin hanci daga hannun wasu ‘yan kwangila na kusan dala miliyan biyar.
Inda majalisar Jiha karo ta 8 ta kafa kwamiti domin gudanar da bincike kan wannan al’amari, sai dai majalisar ba kai ga kammala bincikenta ba, sai ga umarni daga babbar kotun jiya dake ƙalubalantar majalisar kan ba ta hurumin gudanar da bincike kan laifin da ake zargin gwamnan.
Don haka, wannan ƙungiya ke jan hankalin hukumar EFCC kan cewa al’ummar jihar Kano na da sha’awar sanin gaskiyar wancan al’amari.
Wannan tasa wannan ƙungiya ke roƙon hukumar EFCC da ta gaggauta cafke gwamnan tare da gudanar da bincike da miƙa shi zuwa kotu domin zama izina ga gwamnoni da ke tunanin suna da kariya wajen kaucewa wa aikata ɓarna makamanciyar wacce ake zargin gwamnan da aikatawa.