Majalisar Tattalin Arzikin Najeriya NEC ta ba da shawarar a bayar da tallafi ga ma’aikata da marasa galihu don rage raɗaɗin cire tallafin mai a ƙasar nan.
Gwamnan jihar Bauchi Bala Mohammed ne ya bayyana haka ga manema labarai jim kaɗan bayan kammala taron ƙaddamar da majalisar wadda mataimakin shugaban ƙasa Sanata Kashim Shettima ke jagoranta.
Majalisar ta bayar da shawarar ne bayan da shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya umarce ta da ɓullo da hanyoyin rage raɗadin.
Gwamnan ya ce majalisar ta yi la’akari da shawarwarin da Hukumar Kula da Albashi da Ma’aikata ta Kasa ta bayar na biyan Naira biliyan 702 a matsayin alawus-alawus na rayuwa ga ma’aikatan gwamnati a wani ɓangare na rage raɗadin.
A lokacin taron majalisar, an kafa wani kwamiti da zai gudanar da aiki, cikin makonni biyu, don yin nazarin hanyoyin da za a bi wajen raba kayan agajin.