A yau ne yarjejeniyar tsagaita wuta da shugaban rundunar dakarun RSF ya sanar za ta fara aiki domin bukukuwan babbar sallar Idi da za a fara ranar Laraba.
An bayar da sanarwar dakatar da rikicin ne a wani sakon murya da aka watsa a gidan talabijin, wanda shugaban kungiyar RSF, Muhammad Hamdan Dagalo, ya gabatar.
Ya ce matakin zai yi aiki ne a ranakun Talata da Laraba.
Janar Hemedti ya kuma yi Allah-wadai da cin zarafi da ake yi wa fararen hula – ciki har da wadanda sojojinsa ke yi.
Ana zargin kungiyar ta RSF da aikata laifukan cin zarafin mutane a Darfur.