‘Dan majalisa mai wakiltar mazabar Pankshin da Kanke da Kanam a majalisar tarayya daga jihar Filato Yusuf Gagdi, ya gwangwaje ‘yarsa Aisha da sabuwar motar alfarma ta gani da fada.
Gagdi ya sayawa diyar motar ne domin murnar kammala karatun makarantar sakandire da kuma samun maki mai kyau a jarrabawar sharar fagen shiga jami’a JAMB
- Gwamnatin Kano Za Ta Dasa Bishiyoyi Dubu 10 A Kowace Karamar Hukuma
- Hisbah A Jihar Katsina Ta Lalata Barasar Naira Miliyan 60
Aisha Gagdi ta kammala karatunta a makarantar Lead British International School Abuja a ranar Asabar.
Wani ma’abocin Facebook, Saminu Maigoro ne ya wallafa hotunan yarinyar da mahaifinta a cikin motar.