Darajar naira ta faɗi a kasuwar harkokin zuba jari da fitar da kayayyaki ta Najeriya, inda ake canzar da dala ɗaya a kan N702.19 ranar Alhamis, a cewar kamfanin dillancin labarai na Najeriya, NAN.
Darajar naira ta ragu da kashi 5.75% idan aka kwatanta da yadda aka canzar da dala ɗaya a kan N664.04 ranar Laraba.
Kanfanin Dillancin Labaran NAN Ya ba da rahoton cewa, an buɗe kasuwar hada-hadar canjin kuɗin a N658.50 kan duk dala ɗaya a ranar Alhamis.
Sai dai dala ɗaya ta kai ƙololuwar farashin N791 yayin hada-hadar ranar Alhamis, kafin ta daidaita a N702.19.
Haka zalika yayin ciniki a ranar Alhamis a wata gaɓa, darajar naira ta tashi inda aka sayar da dala ɗaya a kan naira 461.
An sayar da jimilar dala miliyan 70.72 a kasuwar harkokin zuba jari da fitar da kaya ta hukuma a ranar Alhamis.