Home » EFCC Ta Cafke Ɗan Tsohon Shugaban Jam’iyyar PDP, Mamman Ali

EFCC Ta Cafke Ɗan Tsohon Shugaban Jam’iyyar PDP, Mamman Ali

by Anas Dansalma
0 comment

Hukumar da ke Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa EFCC ta sake gurfanar da Mamman Ali, ɗa ga tsohon shugaban jam’iyyar PDP na ƙasar Ahmadu Ali, bisa zargin zambar naira biliyan 2.2 na tallafin man fetur.

Kamfanin dillancin labaran ƙasar NAN, ya ruwaito cewa an sake gurfanar da Mamman Ali tare da wani mutum mai suna Christian Taylor da kamfanin mai na Nasaman Oil Services Ltd. a gaban wata kotu a birnin Legas.

An gurfanar da su ne bisa zarge-zagen laifuka 49 ciki har da haɗa baki, da yaudara da zamba cikin aminci, da yin ƙarya domin karɓar kuɗi da amfani da takardun bogi.

Sai dai sun musanta duka zarge-zargen da ake yi musu.

Lauyan hukumar EFCC Samuel Atteh, ya nemi kotun da ta sanya ranar sauraron ƙarar ta yadda zai gabatar da shaidunsa da za su tabbatar da zargin da hukumar ke yi wa mutanen.

Sai dai lauyan waɗanda ake zargin Kolade Obafemi ya nemi kotun da ta bayar da belin waɗanda yake karewa.

Daga ƙarshe alƙalin kotun ya bayar da umarnin cewa waɗanda ake zargin su ci gaba da kasancewa a hannaun hukumar ta EFCC har zuwa lokacin da za a gabatar da takardun neman belinsu a hukumance.

Alƙalin ya kuma ɗage sauraron ƙarar har zuwa ranar 30 ga watan Mayu mai zuwa.

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai mai cikakkiyar rajista wadda manufarta ita ce ilimantarwa, da wayar da kai da Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.
Muna nan a kan titin Guda Abdullahi gida mai lamba 19 a Farm Centre, jihar Kano.

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi

©MuhasaTVR 2023. Ku nemi izini kafin yin amfani da duk abin da aka wallafa a wannan shafi

Are you sure want to unlock this post?
Unlock left : 0
Are you sure want to cancel subscription?