Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashgawa EFCC ta kama Daraktan Kudi ta Hukumar Harkokin Jiragen Sama Bilkisu Sani tare da wasu jami’An hukumar su uku bisa zargin badakalar kudin hutu har naira biliyan 2.
Sauran mutanen uku da aka kama tare da daraktan su ne mataimakin babban daraktan hukumar Hart Benson Fimienye, da mataimakin daraktan kudi na hukumar Obene Jenbarimiema Turniel, sai kuma manajan da ke kula da bangaren ajiye-ajiye na hukumar Nathaniel Terna Kaainjo.
Ana dai zargin daraktan da sauran mutanan uku ne da biya wa kansu kudaden tafiye-tafiye har naira biliyan biyu wanda hukumar ke zargin ya saba ka’ida.
Majiyarmu ta ruwaito cewar, jami’in hukumar ya ce an kama Nathaniel ne tun 16 ga watan nan a yayin da sauran mutanen suka shiga hannu a jiya litinin, kuma a yanzu haka suna shedikwatar hukumar ta EFCC da ke Abuja.