Fadar gwamnatin Najeriya ta nemi afuwa kan iƙirarin da ta yi na cewa shugaba Bola Ahmad Tinubu shugaban Afirka na farko da ya fara rufe hada-hadar Cinikayyar Hannun Jari na NASDAQ da ke ƙasar Amurka.
A ranar Talatar da ta gabata ne, mai magana da yawun shugaban ƙasa, Ajuri Ngelale, ya fitar da wata sanarwa da ta ayyana Tinubu a matsayin shugaba na farko a Afirka da ya samu wannan karramawa.
Sai dai rahotanni sun tabbatar da cewa, tsohon shugaban Tanzania, Jakaya Kikwete, ne ya fara rufe cinikayyar hannayen jarin a shekarar 2011.
Ranar Juma’a, fadar shugaban Nijeriya ta nemi afuwa bisa waɗancan kalamai tare da cewa sun yi su ne bayan samun bayanai daga ɗaya daga cikin masu shirya wannan taro.