Gamayyar masu saka ida a zaben 2023 sun bukaci Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), da ta sake yin nazari kan sakamakon zaben Jihar Kaduna.
Masu saka idon kan zabe dai sun ce zaben ya yi kyau a Jihar Kaduna, amma a wajen tattara sakamakon zaben bai yi daidai da abin da aka dora a safin INEC ba.
A wani taron manema labarai da aka gudanar a Abuja, babban jami’in cibiyar kula da da’a da dabi’u na kasa, Roman Azubuike, wanda ya yi magana a madadin jami’in hukumar INEC, ya ce ya kamata hedkwatar INEC ta kasa ta sake duba sakamakon zaben gwamnan Kaduna. Jami’in kula da zaben gwamnan Jihar Kaduna, Farfesa Lawal Bilbis, ya bayyana cewa dan takarar jam’iyyar APC, Uba Sani ya samu kuri’u 730,002, inda ya doke abokin takararsa Isah Ashiru na jam’iyyar PDP wanda ya samu kuri’u 719,196.
AZUBUIKE YACE SUNA kira ga INEC da ta sake duba sakamakon zaben gwamnan Jihar Kaduna.
ya kara da cewa Zaben ya kasance a bayyane har zuwa lokacin fara tattara sakamakon zabe al’amura suka fara canzawa. Tun farko dai tsarin ya kasance a bayyane, amma a Kudancin Kaduna da Birnin Gwari da wasu kananan hukumomi ya kamata a sake yin nazari a kansu saboda ba a tura sahihin sakamakon zaben zuwa shafin INEC a kan lokaci ba.
“Don haka suuna amfani da wannan dama wajen yin kira ga INEC da ta sake duba sakamakon zaben, musamman zaben gwamna,