Gwamantin Jihar Kano ta sanar da janye dokar hana zirga-zirga da ta sanya a safiyar jiya Litinin bayan sanar da sakamakon zaben gwamna da na ’yan majalisar jihar.
Gwamnatin Kanon ta sanya dokar hana fita ne a jihar da nufin kauce wa tabarbarewar doka da oda biyo bayan bayyana sakamakon zaben gwamna da na ‘yan majalisar dokokin jihar.
Kwamishinan yada labarai da harkokin cikin gida na Kano, Muhammad Garba, shi ya sanar da dage dokar a cikin wata sanarwa da ya fitar a daren jiya.
Ya ce gwamnatin ta dage dokar bayan ta yi nazari sosai kan lamarin da kuma kwanciyar hankali da ya wanzu a fadin jihar.
Kwamishinan ya yi kira ga bankunan kasuwanci da ma’aikatan gwamnati da sauran al’ummar jihar da su fito su ci gaba da sana’o’insu na yau da kullum.