Kwamishinan Lafiya na Jihar Kano, Dr. Abubakar Labaran Yusuf, ya yi kira ga sauran ƙananan ma’aikatu da ke ƙarƙashin Ma’aikatar Lafiya ta jihar da su yi koyi da Gidauniyar Lafiya ta Kano ( KSCHMA).
Kwamishinan ya yi wannan kira ne a lokacin taron wayar da kai na kwanaki 3 da gidauniyar tare haɗin guiwar shirin nan na lafiya wanda aka yi domin inganta tsarin ayyukan gidauniyar lafiyar.
A cikin jawabin da ya yi, babban sakatariyar gidauniyar lafiya ta Kano, Dr. Rahila Aliyu Mukhtar, ya ce, gidauniyar lafiyar ta himmatu ne wajen samar da tsarin da zai taimaka wa ‘yan jihar wajen samun sauƙin biyan kudaɗe neman lafiya.
Dr. Rahila ta bayyana cewa taron wayar da kan zai mai da hankali ne wajen samar da tsarin da zai taimaka waɗanda suke cikin shirin gidauniyar lafiyar.
Ta ce, wannan tsari zai kawo ƙarshen yankewar magunguna a faɗin jihar nan.inda a ƙarshe ta yaba wa masu ɗaukar nauyin, da masu ruwa da tsaki da duk wadanda ke cikin shirin tare da yin alƙawarin samar da duk abin da al’umma ke buƙata da a da babu su.