Home » Gobara ta Ƙone Wasu Rumfuna da Dama a Kasuwar Rimi da ke Jihar Kano

Gobara ta Ƙone Wasu Rumfuna da Dama a Kasuwar Rimi da ke Jihar Kano

by muhasa
0 comment

Wata gobara ta tashi a kasuwar Rimi da ke Kano, inda ta ƙone shaguna sama da 19 a cewar Kanfanin Dillacin Labarai ta Ƙasa (NAN).

Wannan al’amari ya faru ne a daren jiya Laraba da misalin 1: 46, a cewar Kakakin Hukumar Kashe Gobara ta ƙasa, Alh. Saminu Abdullahi.

A cewarsa ku san shaguna 14, da wasu guda biyar da masallaci guda ɗaya suka ƙone ƙurmus.

Sai dai ya bayyana cewa babu wani rahoton game da wani da ya samu rauni a yayin wannan gobara.

Sannan har izuwa yanzu ba a kai ga gano dalilin da ya assasa wannan gobara ba, domin haka hukumar tasu tana nan tana cigaba da gudanar da bincike a kan haka.

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai dake da cikakkiyar rejista da ke da manufa ta ilimantarwa, wayar da kai Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.

Ofishinmu yana nan a kan titin Guda Abdullahi dake Farm Centre a jihar Kano. 

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi