Gobara ta tashi a cikin wani gini da ake kira White House a baban kasuwar Onitsha dake jihar Anambra.
Gobarar ta tashi ne a sashen dakin ajiyar kaya na Gbongoro, wanda ya kasance waje ne a bayan kasuwar da ake sayar da tufafi kamar yadudduka da sauran kayayayakin sakawa.
Karanta Wannan: Gamnatin Jihar Kano Ta Janye Dokar Hana Zirga-zirgar Ababen Hawa
Mahukun dai suna nan suna nazarin musabbabin tashin gobarar da aka wayi gari da ita a safiyar yau Talata.
Gobarar dai ta janyo asarar kayayaki na milliyoyin Naira.
‘Yan kasuwar na kokarin kashe gobarar yayin da wasu kuma ke ci gaba da kiran jami’an kashe gobara.
Shedun gani da ido sun bayyana cewar gobarar ta tashi a gurin da ake siyar da kayayyakin dinki na White House, wanda a ƙa’ida wajen ajiyan motoci ne da fitar gaggawa amman ‘yan kasuwar suka toshe hanyar da shaguna na wucin gadi.