Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da , sakataren yada labaran jam’iyyar APC na jihar MOSES KYARI, ya sanyawa hannu ranar Asabar a Gombe.
Kyari ya ce jam’iyyar ta kuma dakatar da dan majalisar wakilai Yunusa Abubakar mai wakiltar mazabar Yamaltu-Deba a majalisar dokokin tarayya bisa zargin yi wa jam’iyyar zagon kasa.
Ya ce shugabannin mazabarsu sun dakatar da ’yan majalisar ne bayan an same su da aikata laifukan cin hanci da rashawa a lokacin zaben 2023 a jihar.
Kyari, ya ce shugabannin Unguwar Bambam da ke karamar hukumar Balanga ne suka dakatar da Sanatan.
Kyari, ya ce an kafa kwamitin da zai binciki lamarin inda ya ce kwamitin ya gayyaci Sanatan amma bai iya kare kansa daga zargin ba don haka kwamitin ya ba da shawarar dakatar da shi daga jam’iyyar.